Rasha ta jaddada kudurinta na ci gaba da taimakawa Mali kan lamuran tsaro

15
Rasha ta jaddada kudurinta na ci gaba da taimakawa Mali kan lamuran tsaro
Rasha ta jaddada kudurinta na ci gaba da taimakawa Mali kan lamuran tsaro

Africa-Press – Mali. Ma’aikatar harkokin wajen Mali ta ce Rasha ta jaddada goyon bayanta ga kasar, bayan kawo karshen aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar.

A sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta ce ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ne ya bada tabbacin hakan.

Tun bayan kulla alaka tsakanin gwamnatin sojin Mali da Rasha, kasar ta bukaci rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MUNISMA ta fice daga cikinta.

A ranar 16 ga watan Yunin da ya gabata ne dai ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya mikawa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya bukatar ficewar rundunar daga kasar.

Rundunar ta MUNISMA na da sansanoni daban daban da ta samar a kasar, tun bayan kafata a shekarar 2013, da zummar taimakawa kasar wajen yaki da masu ikirarin jihadi.

Ruwa ya yi tsami tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Mali tun bayan juyin mulkin shekarar 2020, da ya maido da gwamnatin sojin da ta yi watsi da alakar tsaron da ke tsakanin kasar da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka.

Pour plus d’informations et d’analyses sur la Mali, suivez Africa-Press

LAISSER UN COMMENTAIRE

Please enter your comment!
Please enter your name here